Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da umarni ga dukkanin ƙananan hukumomi 44 da ke jihar da su bayar da gudunmawar N15,227,272.72 kowanne, wanda gaba ɗaya ya kama N670 miliyan, domin gyaran wasu tsofaffin motoci da kuma sayen sababbi ga Fadar Masarautar Kano, kamar yadda wata wasiƙa daga Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi ta tabbatar.
Wasiƙar mai lamba MLG/INSP/LGD/166T/6 ta ranar 25 ga Maris, 2025, an aika ta ga dukkan shugabannin ƙananan hukumomin jihar, inda aka bayyana cewa za a cire kuɗin daga asusun haɗin gwiwa tsakanin jiha da ƙananan hukumomi.
Wani jami’in fadar sarki da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar wa da jaridar PUNCH da ingancin wasiƙar, yana mai cewa, “Kamfanin da zai kawo motocin da gyara tsofaffin tuni an tuntuɓe shi, kuma shirin na tafiya.”
KARANTA WANNAN: Yanda Za A Duba Sakamakon JAMB Ta 2025
Wasiƙar da Daraktan Binciken Ƙananan Hukumomi, Abubakar S. Dabo, ya sanya wa hannu a madadin Kwamishinan Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi, ta ƙara da cewa za a gyara motar 1993 Fleetwood Cadillac Limousine da Daimler D5 420 1998 kowacce a kan N25m, sannan a sayi sabbin motoci guda huɗu da suka haɗa da Toyota Hilux 2024 (N98m), Toyota Hiace Bus (N98m), Toyota Land Cruiser VXR full option 2024 (N268m), da kuma Prado 2024 (N156m).
Jaridar PUNCH ta kuma gano cewa wasiƙar ta yi wa mai binciken kuɗaɗe na ƙananan hukumomi da sauran jami’an bincike na ma’aikatar kwafin takardar, tare da buƙatar a bi matakan da suka dace kafin aiwatar da shirin.
Sai dai wannan matakin ya jawo martani daga ɗan siyasar APC, Alhaji Alhassan Yaryasa, wanda ya ce, “Yaya gwamnati za ta ware irin wannan kuɗi mai yawa a lokacin da jama’ar birnin Kano da wasu manyan garuruwa ke fama da rashin ruwa?”
A cewarsa, wannan mataki ne na rashin bayar da fifiko ga abin da ya dace, yana mai cewa, “Sarki Sanusi bai buƙatar sabbin motoci masu tsada; ina na baya da ya dawo da su?”
Yaryasa ya nemi Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya janye wannan ƙuduri, yana mai cewa, “Kano za ta tuna da wannan rashin adalci, musamman ganin yadda ɓangarorin ilimi da lafiya ke neman agaji fiye da kowane lokaci.”