Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ƙungiyar WAMY Zata Gina Jami’ar Musulunci A Jigawa

Ƙungiyar Taron Matasa Musulmi ta Duniya, WAMY, ta yi alƙawarin gina gagarumar jami’ar Musulunci a Jihar Jigawa.

Wannan ƙudiri na WAMY ya bayyana ne lokacin Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi ya ziyarci ofishin ƙungiyar da ke Kano a jiya Asabar.

Daraktan ƙungiyar, Hashem Mohammed Abdelsalam ya yabawa Gwamna Namadi bisa ziyarar, inda ya ce shine gwamna na farko a tarihi da ya ziyarci ofishin ƙungiyar.

Ya bayyana cewa, ƙungiyar WAMY ta zo Najeriya ne a shekarar 1973, shekara ɗaya bayan kafata, kuma tun wannan lokacin take aiwatar da aiyukan jin ƙan al’umma musamman a yankin Kudancin Najeriya.

Ya ƙara da cewa, a shekarar 2000 ne wani ɗan Jihar Jigawa ya baiwa ƙungiyar kyautar fili a Kano, abin da ya ba ta damar gina ofishinta a Kanon.

Ya ce a ƙoƙarin ƙungiyar na bunƙasa ilimin al’umma, ta yanke shawarar samar da jami’ar Musulunci a Jihar Jigawa, ganin yanda ta samu nasarar kafa irinta ta Alhikmah University, Ilorin a Jihar Kwara.

Gwamna Namadi ya tabbatarwa ƙungiyar samun haɗin kan gwamnatinsa domin ganin ta cimma burinta a Jihar Jigawa.