Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ƴan Najeriya Na Roƙon Ƴan Ƙwadago Da Su Bar Wutar Lantarki A Lokacin Yajin Aiki

A daidai lokacin da dambarwa ke cigaba da ƙamari tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago da Gwamnatin Tarayya kan mafi ƙarancin albashi, ƴan Najeriya sun shiga shafukan sa da zumunta domin roƙar ƴan ƙwadagon da kar su katse wutar lantarki a lokacin yajin aikin da ake tunanin komawa.

A yau Litinin ne, ƙungiyar ƙwadago ta NLC tai watsi da tayin da gwamnati tai na naira 62,000 ko naira 100,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, inda Mataimakin Babban Sakataren NLC, Chris Onyeka ya bayyana tayin a matsayin tayin talauci.

Ya ce matsayarsu tana nan kuma a bayyane take, saboda haka ba zasu taɓa yarda da duk wani tsari na ƙara sanya ƴan Najeriya a cikin yunwa ba.

Onyeka ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da gidan Talabijin na Channels a yau Litinin.

Ƙungiyar NLC dai ta tsaya kan matsayarta na neman mafi ƙarancin albashi na naira 250,000 wanda ƙungiyar ke ganin ta yi la’akari da aljihun gwamnatoci a Najeriya.

A yajin aikin da ƙungiyar NLC ta jagoranta a makon da ya gabata, ƴan Najeriya da dama sun koka kan matsalar rashin wutar lantarki wadda ƙungiyar ta katse, abun da ya sa a wannan karon, suka garzaya shafukan sa da zumunta domin roƙon ƴan ƙwadagon da su ƙayale wutar a wannan lokacin.