Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Masu Fyaɗe 5 Sun Yi Lalata Da Ƙaramar Yarinya A Jigawa, Ɗaya A Cikinsu Yana Da Ƙanjamau

Jami’an ƴansanda a Jigawa sun cafke mutane biyar da ake zargi da yin lalata da ƴar ƙaramar yarinya ƴar shekara 14, inda aka samu ɗaya a cikinsu ɗauke da ciwon ƙanjamau.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ƴansandan Jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam ne ya tabbatar da labarin ga manema labarai a jiya Litinin.

Ya ce, a ranar Juma’a, 28 ga watan Yulin da ya gabata ne da misalin ƙarfe 10 na dare wata ƙwaƙƙwarar majiya ta bayyana cewa, a wannan ranar da misalin ƙarfe 8:30 na dare, wata yarinya ƴar shekara 14 da take tallen awara, yayinda wani mai suna Aliyu Sani mai shekaru 50 a duniya ya yaudareta zuwa ɗakin wani mai suna Rabiu Ibrahim mai shekaru 45 suka yi lalata da ita.

DSP Shiisu ya ƙara da cewa, binciken da aka gudanar a ofishin SCID da ke Dutse ya nuna cewar, wani da ake kira da Idris Haruna ɗan shekara 38, da wani da ake kira da Rabiu Inuwa ɗan shekara 50 da kuma wani mai suna Hussaini Mato ɗan shekara 32 su ma sun aikata lalata da yarinyar a lokuta da dama a ranaku mabanbanta da gurare mabanbanta.

Jami’in ƴansandan ya ce, dukkan mutane biyar ɗin da ake zargi ƴan asalin Ƙaramar Hukumar Jahun ne da ke Jihar Jigawa.

An kai dukkan waɗanda ake zargin da kuma yarinyar Cibiyar Kula da Waɗanda Aka Ci Zarafi ta Dutse, SARC, domin binciken lafiya, yayinda aka gano ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin na ɗauke da cutar ƙanjamau, HIV, sannan kuma aka samu ɗaya da ciwon hanta, sai dai an yi dacen samun yarinyar cikin ƙoshin lafiya.

DSP Lawan Shiisu Adam ya ce, za a miƙa waɗanda ake zargin zuwa kotu domin ɗaukar matakin da ya dace a kansu.