Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Fitar Da Jerin Buƙatunta Guda Bakwai, Ta Jaddada Buƙatar Sabon Mafi Ƙarancin Albashi

Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya, NLC ta fitar da jerin buƙatun da take da su ga Gwamnatin Tarayya a daidai lokacin da ake tunkarar Ranar Ma’aikata wato 1 ga watan Mayu.

Baya da neman sabon mafi ƙarancin albashi, NLC na kuma buƙatar a samar da ƴansandan jihohi da na ƙananan hukumomi domin magance matsalar tsaro.

Ƙungiyar kuma ta jaddada cewar dole ne gwamnatocin jihoi da na ƙananan hukumomi da kamfanoni masu zaman kansu su biya mafi ƙarancin albashi lokacin da aka aminta da shi.

Ana sa ran cewar, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai sanar da sabon mafi ƙarancin albashi a jawabinsa na ranar ma’aikatan, abun da ƙungiyar ƙwadagon ke fatan ya kai naira 615,000 a kowanne wata.

A ranar 18 ga watan Afrilu na shekarar 2019 tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan mafi ƙarancin albashi na naira 30,000 kowanne wata, yayin da a tsarin doka ya zo ƙarshe a ranar 18 ga watan Afrilun bana, hakan kuma ke nuna matuƙar buƙatar sabon mafi ƙarancin albashin a kwanakin nan.