Ƙungiyar Manoman Najeriya (AFAN) reshen Jihar Jigawa ta bayyana ɓacin ranta kan rahotannin da ke nuna wasu ƴan damfara da ke karɓar kudi daga hannun manoma suna fakewa da shirye-shiryen tallafin noma na bogi.
A cikin wata sanarwa, Shugaban AFAN na jihar, Injiniya Auwal Garba Ibrahim, ya yi alƙawarin gano waɗanda ke da hannu a wannan aikin domin gurfanar da su gaban doka.
Ya gargaɗi manoma da su kasance masu lura sosai kuma su kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba ga ƙungiyar ko hukumomin tsaro.
“Ina mai jaddada cewa mun lura da yadda wasu ƴan damfara ke fakewa da sunan shugabannin AFAN suna karɓar kuɗi daga manoma suna cewa na rajistar tallafin noma na musamman ne. Wannan shirin da suke faɗa yaudara ce kuma ba ya faruwa,” in ji shi.
Injiniya Auwal ya bayyana cewa wannan aiki na damfara na iya haddasa rashin amincewa tsakanin manoma da shugabanni, wanda hakan zai iya kawo cikas ga manufofin noma na jiha da tarayya.
“Muna son yin bayanin cewa Ƙungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN), reshen Jihar Jigawa, ba ta da irin wannan aiki. Ba mu taɓa karɓar kuɗi daga manoma don wani tallafi daga Gwamnatin Tarayya, Jiha, ko wata ƙungiya ba. Muna Allah-wadai da wannan ɗabi’a marar kyau da rashin tausayi. Waɗanda ke da hannu a wannan aikin ba shugabanni ko wakilanmu ba ne.”
AFAN ta buƙaci manoma su ci gaba da kula da tsaron kansu tare da kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba ga hukumomi ko ofisoshin ƙungiyar.
“Muna kira ga kowa da ya kasance mai lura domin kare martabar shirye-shiryen noma a Jihar Jigawa,” in ji sanarwar a ƙarshe.