Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ƙungiyar Yarabawa Ta Matsa Kan Samar Da Ƴansandan Jihohi Da Gudanar Da Cikakkiyar Fedaraliya

Ƙungiyar Yarabawa ta Afenifere ta koka kan yawaitar matsalar tsaro a wasu sassa na ƙasar nan saboda hare-haren wasu makiyaya masu ɗauke da makamai kan manoma.

Ƙungiyar ta bayyana cewar, munanan aiyukan laifin da ƴanbindigar ke aikatawa a kan manoma ya jawo ƙarin buƙatar samar da ƴansandan jihohi domin inganta tsaro tun daga tushe.

Wannan kira na ƙungiyar na ɗauke ne a cikin sanarwar bayan taro da Babban Sakataren Ƙungiyar, Chief Sola Ebiseni ya rabawa manema labarai a jiya Laraba a Ogbo Ijebu ta Jihar Ogun.

Ƙungiyar ta ƙara jaddada adawarta da yin kiwo a buɗe kamar yanda aka saba, sannan kuma ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta yi amfani da rahoton Taron Ƙasa na 2014 ko kuma rahoton Kwamitin Nasir El-Rufai kan samar da cikakken tsarin fedaraliya domin gyara kudin tsarin mulkin Najeriya na 1999.