
Yayin da ake ci gaba da yaƙin farashi a kasuwar man fetur a Najeriya, dillalan mai sun rage yawan sayen mai domin gujewa asara sakamakon ci gaba da saukar farashin man.
Yaƙin farashin ya fara ne tun a watan Nuwambar 2024, lokacin da kamfanin Dangote Refinery ya rage farashin litar man fetur daga N990 zuwa N970, sannan daga baya ya kara ragewa zuwa N825 har ma zuwa N815 a makonnan.
NNPCL ma ya bi sawu shima, inda ya rage farashin nasa, lamarin da ke kara tsananta gasa a kasuwar man fetur.
Duk da cewa ƴan Najeriya na cin moriyar wannan farashin mai sauki, masana sun bayyana cewa ƴan kasuwa na fuskantar asarar sama da naira biliyan 75 a kowanne wata.
Shugaban ƴan kasuwar man fetur (IPMAN), Hammed Fashola, ya bayyana cewa sauƙar farashin na janyo wa ƴan kasuwa asara, wanda ya sa suke rage yawan man da suke siya domin gujewa ƙarin asara.
“Abin da ya kamata shi ne a duba yadda za a samu daidaiton farashin mai, domin ƴan kasuwa suna shiga matsala idan farashin ya riƙa sauƙa ba zato ba tsammani,” in ji Fashola.