Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ƴansanda Sun Ceto Waɗanda Aka Yi Garkuwa Da Su, Sun Kuma Kashe Ƴanbindiga

Jami’an ƴan sanda a jihohin Abia da Nasarawa sun ceto mutane huɗu da aka sace, tare da kashe ƴanbindiga bakwai a farmakin da suka kai. 

Kakakin rundunar ƴansanda na ƙasa ya bayyana cewa, a Abia, an kai farmaki a maboyar ƴanbindiga a Osokwa, Osisioma, inda aka yi artabu da su, kuma aka ceto mutane huɗu ba tare da samun wata illa ba.

A Nasarawa kuwa, jami’an tsaro sun kashe wani shahararren ɗanbindiga mai suna Abdullahi, wanda aka fi sani da “Honor,” yayin wani samame da suka kai tare da hadin gwiwar sojoji da ƴan vigilante. 

An samu makamai da alburusai a hannun ƴanbindigar, yayin da ɗaya daga cikinsu ya tsere da raunin harbi a jikinsa. 

Babban Sufeton ƴansanda na kasa, Kayode Egbetokun, ya jinjinawa jami’an da suka gudanar da farmakin, tare da jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da fatattakar masu aikata laifi a ƙasar.