Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ƴansanda Sun Kama Ɓarayin Babura A Bauchi

Jami’an ƴansanda a Jihar Bauchi sun sami nasarar kama wasu mutane guda biyu waɗanda ake zargi da sun ƙware wajen ƙwatar babura daga masu su a yankin Gudum Hausawa da ke jihar.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ƴansandan Jihar Bauchi, Ahmed Wakil ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labari a jiya Lahadi a Bauchi.

Ahmed Wakil ya ce, yaudarar da waɗanda ake zargin suke yi ita ce, su buƙaci ɗan acaɓa da ya kai su wani waje, sannan lokacin da suke tafiya sai su farmake shi, su ƙwace babur dinsa.

Ya ce, a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli, jami’an ƴansanda sun sami nasarar kama Mustapha Adam ɗan Unguwar Mahaukata da Jafar Lawan ɗan Unguwar Gudun Hausawa a Bauchi, inda sukai basaja a matsayin fasinjoji sannan suka farmaki wani ɗan acaɓa mai suna Kabiru Muhammad ɗan Unguwar Magaji da nufin ƙwace masa babur dinsa.

Waɗanda ake zargin sun ce Kabiru ya kai su filin jirgi daga Babbar Kasuwa, sannan yayin da suka kai yankin Wikki sai suka zaro sifanar babbar mota suka ƙwala masa a ka, abin da ya sa ya faɗi a sume.

Ƴansanda sun kai ɗauki wajen da suka sami rahoto, sannan suka garzaya da Kabiru Muhammad zuwa asibiti, daga bisani kuma suka bi masu laifin suka kama su a tsakiyar garin Bauchi.