Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ɗaliban Jami’o’i Da Manyan Makarantu Sun Koka Kan Rashin Samun Bashin Karatu Na NELFUND

Ɗalibai daga jami’o’i da manyan makarantu (polytechnics) sama da 23 sun nuna damuwa kan jinkirin da ake samu wajen rabon bashin karatu daga Asusun Bashin Ilimi na Ƙasa (NELFUND).

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya rattaba hannu kan dokar bai wa ɗalibai bashin karatu a ranar 3 ga Afrilu, 2024, domin tabbatar da ingantaccen tallafin ilimi ga ƴan Najeriya.

Har zuwa ranar 3 ga Fabrairu, 2025, NELFUND ta bayyana cewa ta karɓi buƙatun neman bashin daga dalibai 364,042 kuma ta raba Naira biliyan 20.07 ga ɗalibai 192,906 domin biyan kuɗin makaranta.

Haka kuma, an fitar da Naira biliyan 12.81 domin tallafin rayuwa ga ɗalibai 169,114, inda kowane ɗalibi ke karɓar N20,000 a kowane wata.

KU KARANTA: JAMB Ta Bayyana Adadin Ƴan Ƙasa Da Shekara 16 Da Suka Yi Rijista A Bana

Sai dai, duk da wannan ci gaban, ɗalibai daga jami’o’i da dama irin su UNN, OAU, Federal University Lokoja, LAUTECH, da Aliko Dangote University of Science and Technology, sun koka cewa har yanzu ba a biya kuɗaɗensu ba, duk da cewa an tantance su tun shekarar da ta gabata.

PUNCH ta rawaito cewa, wani ɗalibi daga Jami’ar Maiduguri, Musty Jr (@JrMusty58254), ya bayyana a shafinsa na X cewa, “Na yi rajista tun watan Agusta amma har yanzu ba a biya ni ba! Don Allah a taimaka kafin Laraba saboda ina cikin matsin rayuwa.”

A Jami’ar Aliko Dangote ta Wudil, Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙungiyar Dalibai, Muhammad Nura, ya fitar da sanarwa yana gargaɗin dalibai cewa idan suka kasa biyan kuɗin makaranta a kan lokaci, hakan na iya kawo musu cikas a jarabawa.

Wani jami’in NELFUND da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Ba matsala ce daga ɓangarenmu ba. Muna aika bayanan ɗalibai zuwa jami’o’i don tantancewa kafin a biya, amma da yawa daga cikin makarantun ba sa bayar da bayanan cikin lokaci.” 

Dalibai da dama sun nemi gwamnatin tarayya da hukumar NELFUND su ɗauki matakan gaggawa domin magance wannan matsala, ganin cewa jarabawarsu na gabatowa.