Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ganduje, Sanwo Olu, Bagudu, Akeredolu Sun Kauracewa Taron Gwamnonin APC Kan Canjin Kudi

Kimanin gwamnoni 10 ne suka halarci muhimmin taron da shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, da shugabannin zartarwa na jihohi suka yi a hedikwatar jam’iyyar ta kasa ranar Lahadi.

Wannan ci gaban na zuwa ne mako guda gabanin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar da aka shirya yi a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.

Gwamna Nasir El-Rufai (Kaduna), Abdullahi Sule (Nasarawa), Muhammad Inuwa Yahaya (Gombe), Mai Mala Buni (Yobe), Abubakar Badaru (Jigawa) da Abubakar Sani Bello (Niger), Yahaya Bello (Kogi), Simon Lalong (Plateau), Biodun Oyebanji (Ekiti), Sani Bello (Niger) da kuma mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa sun halarci taron.

Gwamna Abdullahi Ganduje (Kano), Atiku Bagudu (Kebbi), Babajide Sanwo-Olu (Lagos) da kusan dukkan takwarorinsa na Kudu ba su sami halarta ba, abin da ya taba mahalarta taron.

Haka kuma akwai wakilan gwamnonin jihohin Imo da Katsina wadanda su ma suka halarci taron.

Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan gabanin ganawar tasu ta sirri, Sanata Adamu ya ce, “Ina yi muku barka da zuwa wannan muhimmin taro na gaggawa. Mun samu wani yanayi da ake bukatar a taru a matsayin masu rike da madafun iko na jihohinmu a Najeriya wadanda aka zabe su karkashin tutar babbar jam’iyyarmu ta APC.

“Na yi farin ciki da amsa gayyata da kuka yi. Kuma ni a fahimtata da yawa daga cikin sauran gwamnonin suna kan hanyarsu ta zuwa. Za ku tuna abin da ke faruwa kwanan nan wanda ya wajabta buƙatar wannan gayyata.

“Ba ma son zama a gaban wani ko wasu hukumomi game da abin da ke faruwa a kasar nan a yau kamar yadda ya shafi babbar jam’iyyarmu. Na ga ya fi dacewa a samu duk wadanda suke rike da mukamai masu muhimmanci a jam’iyya, mu hadu a yi mu’amala da juna ta yadda za mu iya samun kyakkyawar fassara da fahimtar halin da muke ciki, wannan shi ne ainihin batun wannan gayyatar.”

Duk da cewa ajandar shirin taron na nuni da ‘Tsarin Sadarwa’ da ‘Shirye-shiryen zaben gama gari’, jawabin shugaban jam’iyyar APC ya yi nuni da cewa tattaunawar kuma za ta kuma karkata kan takun-saka tsakanin shugaban kasa, Muhammadu Buhari da wasu gwamnonin da suka fusata kan manufar sake fasalin Naira.