Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, a yau Talata, ta bayar da Shaidar Cin Zabe ga wadanda suka sami nasarar lashe zabe a ranar 25 ga Fabarairu, 2023 domin zuwa Majalissar Dattawa.
Shugaban Hukumar INEC, Mahmood Yakubu ne ya jagoranci bayar da shaidar a wajen tattara sakamakon zabe da ke International Conference Centre a Abuja.
A ranar Asabar da ta gabata ne, Yakubu ya sanar da cewa an bayyana wadanda suka sami nasara domin zuwa Majalissar Tarayya su 423, abin da ke nuni da cewar za a sake zabe a sauran mazabu 46 na Najeriya.
Wadanda aka bayyana cin zabensu sun hada da ‘yan Majalissar Dattawa 98 cikin 109, da ‘yan Majalissar Wakilai 325 cikin 360.
Karanta Wani Labarin: Wasu Bankunan Sun Fara Sakin Tsoffin Kudi Na Naira 1000 Da 500 Ga Kostomominsu
Jam’iyyu 7 ne suka sami nasarar samun kujeru a Majalissar Dattawa, yayin da jam’iyyu 8 suka samu a Majalissar Wakilai.
Shugaban Hukumar INEC ya bayyana cewa a Majalissar Dattawa, jam’iyyar APC ta samu kujeru 57, PDP ta samu 29, LP ta samu 6, SDP ta samu 2, NNPP ta samu 2, YPP ta samu 1, sai kuma APGA ita ma ta samu 1.
A bangaren Majalissar Wakilai kuma, Jam’iyyar APC ta samu kujeru 162, PDP ta samu 102, LP ta samu 34, NNPP ta samu 18, APGA ta samu 4, ADC ta samu 2, SDP ta samu 2, sai kuma YPP ta samu 1.
Ana sa ran cewa, ranar Laraba mai zuwa za a bayar da shaidar cin zaben ga wadanda suka sami nasara a bangaren Majalissar Wakilai.