Kotun Ƙolin Najeriya ta umarci hukumar zaɓen ƙasar ta maye gurbin sunan Mallam Ibrahim Shekarau da na Rufa’i Hanga na jamiyyar NNPP, a matsayin sanatan mazabar Kano ta tsakiya.
A hukuncin da mai shari’a Justice Uwani Abba-Aji ta yanke yau Juma’a, kotun ta amince da hukuncin da kotun ɗaukaka kara ta yi a baya, inda ta umarci INEC ta amince da Rufa’i Hanga a matsayin dan takarar jam’iyyar NNPP na mazaɓar a zaɓen ranar 25 ga watan Fabarairu, 2023.
Ita dai INEC ta ayyana shekarau a matsayin wanda ya ci zaben, kasancewar ta ki yarda da janye sunansa da ya yi a matsayin dantakarar NNPP tun da farko bayan da hukumar ta ce lokacin sauya dan takara ya wuce.
Jam’iyyar NNPP ta maye gurbin Shekarau a matsayin dan takara bayan da tsohon gwamnan Kanon ya fice daga jam’iyyar ya koma PDP.
BBC