Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Fadar Shugaban Kasa Ta Tabbatar Da Ajiye Aikin Karamin Ministan Mai

Cecekucen da ya dabaibaye jita-jitar ajiye aikin Karamin Ministan Mai na Najeriya, Timipre Sylva ta zo karshe a Juma’ar nan, bayan Fadar Shugaban Kasa ta tabbatar da cewa Sylva ya ajiye aikinsa.

Mai Taimakawa Shugaban Kasa na Musamman a kan Kafafan Sadarwa na Zamani, Bashir Ahmad ne ya tabbatar da hakan a shafinsa na Twitter, inda ya kara da cewa, Sylva ya ajiye aikin ne domin ya nemi takarar gwamna a jiharsa.

“Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, kuma tsohon Gwamna Jihar Bayelsa, Timipre Sylva, ya sauka daga mukaminsa domin ya tsaya takarar gwamna a zaben da za a gudanar a Bayelsa nan gaba kadan,” in ji Ahmad a shafinsa na Twitter.

Rahotanni dai sun nuna cewa, a tsarin jam’iyyar APC, minista zai ajiye aikinsa ne kwanaki a kalla 30 kafin ranar 14 ga April, 2023 da za a gabatar da zaben fidda gwani na gwamna a jihar Bayelsa, sai dai kuma an ki amincewa da ajiye aikin na Sylva.

“Ni ban ga takardar ajiye aikinsa ba, kuma ba zan iya tabbatar muku da cewa ko ya ajiye aikin. Amma kun san ka’idar jam’iyya ita ce mutum zai ajiye aiki kwanaki 30 ne kafin zaben fidda gwani.

“Saboda haka idan har ya tura takardar ajiye aikinsa ga Shugaban Kasa, ba zan iya tabbatarwa ba, amma dai tabbas ne yana neman gwamnan jihar Bayelsa,” in ji wata kwakkwarar majiya a Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur ta Tarayya wadda ta nemi a boye sunanta.

Sylva ya taba zama gwamnan Bayelsa na tsawon wa’adi guda, tsakanin shekarar 2008 zuwa 2012, lokacin yana dan jam’iyyar PDP.