Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ganduje, El-Rufai, Gbajabiamila Da Sauransu Na Fafutukar Neman Mukami A Gwamnatin Tinubu Yayin Da Shugaban Kasa Mai Jiran Gado Yai Batan Dabo Daga Ganin Mutane

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai yanzu na fafutukar samun matsayi a majalissar Shugaban Kasa mai Jiran Gado, Bola Ahmad Tinubu kamar yanda SaharaReporters ta gano.

Haka kuma cikin masu neman su zama shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa akwai Kakakin Majalissar Wakilai, Femi Gbajabiamila da kuma Ministan Aiyuka da Gidaje, Babatunde Raji Fashola.

A ranar 1 ga watan Mayu ne dai aka baiyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben 25 ga watan Fabarairu bayan ya samu kuri’u mafiya rinjaye da kuma samun kaso 25 a jihohi 29 cikin jihohin da aka yi zaben.

Ya samu nasara a kan Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, Peter Obi na jam’iyyar Labour Party, Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar NNPP da sauran ‘yan takara 14.

A kwanannan ne aka rawaito cewa, Tinubu ya yi tafiya zuwa Turai domin neman lafiya bayan ya kamu da rashin lafiya bayan kammala zabubbuka.

Da yake tabbatar da rahotannin, Shugaban Kasar mai Jiran Gado ya ce, ya yi tafiya zuwa birnin Paris na France, daga bisani kuma zai wuce Birtaniya da Saudiyya domin hutawa da shiryawa karbar mulki.

Tun bayan fitar tasa dai har yanzu ba a gan shi a bainar jama’a ba, sannan ba a da masaniya kan lokacin da zai dawo Najeriya.

WASU LABARAN:

Wata majiya a ranar Juma’ar nan, ta sanar da SaharaReporters cewa, wasu daga cikin gwamnoni masu ci da tsoffin gwamnoni sun nuna sha’awarsu ta samun mukamin minister a gwamnatin Tinubu.

“Gwamnan Kano Ganduje yana son ya zama Ministan Birnin Tarayya Abuja, El-Rufai yana son ya zama Mai Bayar da Shawara kan Harkokin Tsaro, NSA, Fashola da Gbajabiamila kowannensu na son zama Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa.

“Wale Edun na son zama Ministan Kudi yayin da Gwamna Bagudu ke son zama Gwamnan Babban Bankin Najeriya.”

Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta taba bayyana cewa, Bagudu na cikin ‘yan tawagar Abacha wadanda suka yi almundahana da almubazzaranci da dukiyar Najeriya a lokacin mulkin Abachan.

Ana sa ran Tinubu zai mika sunayen ministocinsa ga Majalissar Tarayya cikin kwanaki 60 na farko bayan rantsar da shi.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne, a ‘yan kwanakin baya ya sanya hannu kan dokar da ta bukaci shugaban kasa da gwamnoni da su mika sunayen wadanda zasu nada ministoci ko kwamishinoni ga Majalissar Tarayya ko majalissun jihohi cikin kwanaki 60 da karbar rantsuwa domin samun tabbatarwa.