Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Zamu Gayyaci IPOB Ta Zo Ta Kare Mu A Lagos – Shugabannin Igbo Na Kudu Maso Yamma

Eze Igbo na Ajao Estate da ke Jihar Lagos, Fredrick Nwajagu, ya yi alkawarin gayyatar masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, zuwa Jihar Lagos domin su kubutar da dukiyoyin al’ummar Igbo a jihar.

Nwajagu ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo mai sakan 49 wanda aka yada a Twitter a shafin @DeeOneAyekooto, inda ya ce yunkurin ya zama dole saboda hare-haren da ake kaiwa ‘yan kabilar Igbo a jihar ta Lagos.

Shugaban na Igbo ya bayyan cewa da gaske yake, sannan kuma ya yi kira ga mutanensa da su dau mataki a Lagos ta hanyar rufe harkokin kasuwancinsu domin nuna kin amincewarsu da wulakancin da suke fuskanta daga wadanda ba Igbo ba da ke jihar.

A faifan bidiyon ya bayyana cewa, “Idan ba wata daya ba, to mako biyu, idan ba mako biyu ba, to mako daya, idan ba mako daya ba, tom kwana uku.

“Bari mu ga tsakaninmu da su a wannan jihar. Tun da suna korar mu da mu fice, bari mu rufe (kasuwancinmu) na mako daya ko mako biyu, sai mu ga yanda jihar zata zama.

“Lokacin da Igbo suka tafi Kirsimeti, jihar zama take ba mutane, sai sun jira mu mun dawo, sannan idan mun dawo ne sai jihar ta samu hada-hada, sai ana samun cunkoson motoci sai komai ya dawo cikin hada-hada.

“Yanzu suna neman mu tafi. Ya kamata su dena yi mana barazana da cewar mu koma garuruwanmu. Zamu kawowa zaman lafiya tsaiko, zaman lafiya zai samu tsaiko.

“Idan mun rufe kasuwanninmu, muna da jami’an tsaro a Anambra, ‘yan IPOB, zamu gayyace su, zamu biya su, wannan shine abin da zamu iya yi musu mu basu aiki. ‘Yan IPOB ba su da aiki. Idan muka rofe kasuwancinmu, ‘yan IPOB zasu kula mana da shagunanmu mu biya su. Ya kamata mu fara haka kuma ya kamata mu zama muna da jami’an tsaronmu ko sa dena farmakarmu da tsakar dare, da safe da kuma rana. Nan da nan zasu dena farmakarmu.”