Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Matar Da Ta Dabawa Mijinta Wuka Har Lahira Ta Ce Ba Ta Da Hankali

Babbar Kotun Jihar Ekiti da ke Ado Ekiti, a ranar Alhamis da ta gabata, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare Janet Jegede a matsayin mai babban laifi saboda dabawa mijinta wuka da tai har ya mutu.

An dai gurfanar da Janet ne a gaban Justice Bamidele Omo-toso a ranar 16 ga watan September na shekarar 2020 a kan zargin aikata kisan kai.

Karar ta ce wadda ake tuhumar, “A ranar 17 ga watan November, 2019, a garin Ado Ekiti ta kashe wani da ake kira Kayode Jegede (mijinta) abinda ya saba da Sashi na 316 aka kuma tanadi hukuncinsa a Sashi na 319(1) na Kundin Manyan Laifuffuka na 2012 a Jihar Ekiti.”

Wani dan marigayin, Ayomide, a jawabinsa ga ‘yansanda ya ce, matar baban nasa ta kirashi inda ta nemi da ya zo ya kai marigayin asibiti saboda ta kashe shi.

“Lokacin da koma gida, na samu mahaifina a cikin jini, yana nunfarfashi. Na ka wuka a kirjinsa. Na tambayeta me ya faru, amma amsarta a wani birkice.

“Lokacin da na cire wukar daga kirjinsa, zubar jinin sai ta karu. Na fita waje na kira makwabta suka temaka min muka tafi da shi asibiti. Aka garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Ekiti, inda muna zuwa aka tabbatar da cewa ya mutu.

“Akwai lokacin da matar baban nawa ta ce min na yi masa gargadi da ya dena aikata haramun. Ta yi barazanar zata kashe shi idan ya ki denawa. Na dauka wasa take, har sai da na ga ta kashe babana,” in ji Ayomide.

WANI LABARIN: An Kama Malamin Jami’a Saboda Bukatar Yin Lalata Da Karbar Kudi A Wajen Daliba Don Ba Ta Maki

Dansanda mai shigar da kara ya kira shaidu biyar sannan ya gabatar da bayanan wanda ake tuhuma, da kuma wuka da hotunan gawar mamacin da kuma bayanan shaidun.

To sai dai kuma lauya mai kare wadda ake kara, Emmanuel Adedeji, wanda ya ce, wadda ake zargin tana da matsalar tabin hankali a lokacin da hatsarin ya faru, ya yi kira ga kotun da ta wanke ta a kan dalilan rashin hankali.

A hukuncin da ya yanke, Justice Omotoso ya ce, “An amince cewa duk inda aka samu ikirarin rashin hankali, wadda ake zargi zai kasance a killace a wani waje domin jiran umarnin gaba na hukumomi.

“Saboda haka, ina bayar da umarnin cewa, a killace wadda ake zargi Janet Jegede a gidan gyaran hali da ke kan titin Afao Road, Ado Ekiti har zuwa lokacin da zata samu yafiyar gwamna kamar yanda yake a Sashi na 223 na Aiwatar da Dokar Manyan Laifuka ta 2011.”