Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce, fasinjoji mata uku ne suka rasa rayukansu yayinda fasinjoji 13 suka sami raunuka lokacin da wata motar bus ta haya ta kama da wuta a jiya Talata.
Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, Alhaji Saaminu Abdullahi ne ya tabbatar da faruwar lamarin wani jawabi da ya rabawa manema labarai a Kano.
Ya ce, motar bus din kirar Toyota Hiace mai lamba XE 222 TRN, ta kama da wuta ne a daidai Government Technical College a yankin Karamar Hukumar Nassarawa da ke jihar.
Ya kara da cewar motar na kan hanyarta ne daga Karamar Hukumar Ajingi zuwa Kofar Wambai a cikin Birnin Kano lokacin da ta kama da wuta.
Jawabin ya kuma ce, ma’aikatan kashe gobara sun samu nasarar kashe wutar tare da ceton da dama daga wadanda hatsarin ya rutsa da su.
Saminu Abdullahi ya kuma ce, mata ukun da suka rasa rayukansu sun kone kurmus ta yanda ba a gane su, sannan ya bayyana sunan biyu daga cikinsu da Surayya Umar da kuma Zeenai Babaji.
Ya kara da cewa, sauran fasinjoji sha-ukun da suka samu raunuka an kai su Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.
Shima direban motar mai suna Muhammad Gali dan shekara 35 da yaron motar mai suna Hassan Danladi dan shekara 30 an kubutar da su ba tare da sun samu raunuka ba, yayinda aka mika su ga ‘yansanda domin yin bincike.
Jami’in kashe gobarar ya kuma alakanta faruwar hatsarin da saba ka’idar tuki ta hanyar yin gudun wuce ka’ida da kuma fashewar tayar baya, inda yai kira ga direbobi da su dinga kulawa wajen tuki.
NAN