
Akwai rashin zaman lafiya a kan titin Apapa-Oshodi biyo bayan zargin kisan dansanda da wasu ‘yan acaba da aka fi sani da okada riders suka yi.
An rawaito cewa, akalla bindigu uku mallakin dansandan ake zargin an an kwace.
DAILY TRUST ta rawaito cewa, lamarin ya faru ne a yankin Cele Bus Stop, abin da ya jawo fargaba a yankin.
Wakilin DAILY TRUST wanda yana wajen lokacin da abin ya faru, ya gano jikkatancen dansanda a gefen titi, inda ya kuma ya ga motocin sintiri da ba su gaza biyar ba dauke da jami’an ‘yansanda dauke da makamai suna bibiyar ‘yan acabar a yankin Second Rainbow/Mile 2 a kan titin.
An gano bangaren ‘yan acabar suna wasa da makamai kamar su sanduna, adduna, rodina suna gudun kamun ‘yansanda.