Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Buhari Ya Kori Wata Babbar Jami’ar Gwamnatinsa Daga Aiki

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya soke nadin da aka yiwa Saratu Umar a matsayin Shugabar Hukumar Bunkasa Sanya Hannun Jari ta Najeriya, NIPC, nan take.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ne ya sanar da hakan a jawabin da ya saki a jiya Alhamis a Abuja.

A umarnin da aka baiwa Ministan Ciniki, Masana’antu da Sanya Hannun Jari, Adeniyi Adebayo, shugaban kasar ya yi umarnin cewa, darakta mafi girma a ma’aikatar ta NIPC ne zai maye gurbin Saratu a matsayin riko.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN ya rawaito a baya cewa, Shugaba Buhari ya amince da sake nada Saratu Umar a watan July na 2022 domin yin wani wa’adin na shekaru biyar a matsayin shugabar ma’aikatar ta NIPC.

Saratu dai ta fara rike mukamin shugabar NIPC ne a watan Yuli na shekarar 2014.

NAN