Isra’ila ta ce jiragen yaƙinta sun kai hari kan makaman atilari da makamai masu linzamin da sojin Syria suka harbo.
BBC ta rawaito cewa, tun da fari, kafar yaɗa labaran Syria ta ce an ji ƙarar fashewar wani abu a kusa da birnin Damascus, ya yin da rahotanni ke cewa Isra’ila na kai hare-hare ta sama babu ƙaƙƙautawa a birnin.
Sojojin Isra’ila sun ce sun harbo makaman roka shida kusa da Isra’ila, yayin da wasu suka faɗa tuddan Golan, kuma alhakin duk abin da ya faru a iyakarta ya rataya a kan gwamnatin Syria.
A kwanakin nan, mayakan ƙungiyar Hamas sun yi ta harba makaman roka zuwa Isra’ila daga Falasɗinu da Lebanon, ya yin da ita kuma ke maida martani da luguden wuta ta sama.