Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

INEC Ta Dakatar Da Kwamishinanta Da Ya Sanar Da Zaben Adamawa

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta umarci Kwamishinanta na Jihar Adamawa, Yunusa Ari da ya tsame kansa daga dukkan wasu aiyuka da suka shafi hukumar har zuwa umarni na gaba.

A wata wasika da aka sanyawa hannu ranar Litinin, Sakataren Hukumar, Rose Oriaran-Anthony ya ce, an umarci sakataren hukumar na jihar da ya jagoranci hukumar a Jihar Adamawa nan take.

Wasikar ta ce, “Ina sanar da hukuncin Hukumar (zabe) cewa, kai (Barr. Hudu Yunusa Ari), Kwamishinan INEC na Jihar Adamawa da ka dakatar da kanka daga shiga al’amuran ofishin hukumar har sai ka ji umarni na gaba.

“An umarci Sakataren Hukumar (na Jihar Adamawa) da ya karbi ragamar jagorancin INEC a Jihar Adamawa nan take.”

Shi dai dakataccen Kwamishinan INEC, Ari, ya sanar da cewa Aishatu Dahiru Binani ta Jam’iyyar APC ce ta lashe zaben gwamnan Adamawa wanda aka kammala a ranar Asabar da ta gabata ana tsaka da tattara sakamako.