Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

DA DUMI-DUMI: Motar Da Ta Kwaso ‘Yan Najeriya Daga Sudan Ta Kama Da Wuta

Daya daga cikin motocin bus da ke aikin kwashe ‘yan Najeriya daga birnin Khartoum na kasar Sudan mai fama da rikici zuwa gabar ruwan kasar ta Port Sudan inda zasu bi zuwa kasar Saudiyya ta kama da wuta da sanyin safiyar yau Litinin.

A farkon ranar yau din ne dai da misalin shabiyun dare, motocin bus guda 26 dauke da ‘yan Najeriya suka bar Al Razi zuwa Port Sudan.

Daya daga cikin motocin mai dauke da dalibai ‘yan Najeriya 50 da alamar Katsina 1 a kan hanyarta ta Port Sudan ta kama da wuta saboda tsananin zafin da tayar motar ta yi.

Shugaban Kungiyar Dattawa ‘yan Najeriya a Sudan, Dr. Hashim Idris Na’Allah na daya daga cikin motar da ta kama da wutar, wadda ke dauke da maza 49 da kuma mace guda.

Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 2:30 na dare a agogon kasar Sudan.

Kafin kamawar motar da wuta, direban ya tsaya a daidai wajen bincike na RSF masu adawa da gwamnati, daidai lokacin da tayar motar ta yi bindiga ta kama da wuta, abin da ya jawo motar ma ta kama.

Dukkan fasinjojin da ke cikin motar sun samu tserewa da cikinta ba tare da samun ko rauni ba.

Daga bisani, an mayar da 40 daga cikin fasinjojin motar cikin sauran motocin da ke kwashe daliban, yayinda sauran fasinjojin kuma suka waye tare da direban motar a wajen binciken na RSF.

Sani Aliyu wanda har yanzu yana can Sudan din ya bayyana cewa, daliban da hatsarin ya rutsa da su sun bayyana cewa sojojin sa kai na RSF sun yi matukar kokari wajen temakawa daliban har ma suka ba su shayi da safe kafin su bar wajensu.

Sama da ‘yan Najeriya 1000 ne ake kwashewa daga Sudan wadanda ake bi da su ta hanyar Port Sudan saboda wahalhalun da aka fuskanta a debe kaso na farko ta iyakar kasar Misra.