Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Damar Yin Karatu Kyauta A University of Dundee Da Ke Ingila

Gidauniyar Steve Weston and Trust Scholarship ta dalibai ‘yan Nahiyar Afirka, ‘yan Amurka da ‘yan Asiya ce, wadanda suke son dora a karatunsu a matakin gaba da digiri na farko a University of Dundee.

Damar zata baiwa dalibi ko daliba damar samun a biya masa kudin makaranta duk, da kudin kashewa kimanin Fan na Ingila 12,600 wanda ya kai naira miliyan 7,336,728. Sannan akwai alawuns na Fan 750 da za a baiwa dalibi da zarar ya sauka a UK. Akwai kuma kudin Neman Kwarewa (Internship) da ya kai Fan 580.

Za a rufe karbar application na neman wannan scholarship a ranar 31 ga watan Mayu, 2023.

Domin dacewa da samun damar wannan scholarship din, dalibi ya zama yana da digiri fannin Law, Economics, Geology, Petroleum, ko Mining Engineering wanda ya kai matsayin 2.1.

Dole ne kuma dalibi ya cika dukkan ka’idojin Turanci (English Requirements) na samun gurbin karatu a University of Dundee.

Tsawon lokacin karatun na Masters watanni 12 ne wato cikakkiyar shekara. Sannan kowanne dalibi zai koma kasarsa ta haihuwa da zarar ya kammala karatun.

Kasashen da suka dace da neman wannan scholarship din sun hada da Botswana, Congo (Democratic Republic), Egypt, Ghana, Kenya, Mozambique, Namibia, Nigeria, Senegal, South Africa, Zambia daga Nahiyar Afirka.

Akwai kuma Argentina, Bolivia, Brazil, Chile, Colombia, Guyana, Peru, Suriname, Trinidad and Tobago daga Nahiyar Amurka.

Sai kuma China, East Timor, India, Indonesia, Mongolia, Thailand daga Nahiyar Asiya.

Domin neman wannan scholarship a danna link na gaba: Steve Weston and Trust scholarships (September 2023)