Shugaban Kasa Mai Jiran Gado, Bola Tinubu ya bar Najeriya domin isa nahiyar Turai, kamar yanda mataimakinsa na musamman ya bayyana.
A wata sanarwa da aka saki a yau Laraba, masu temakawa shugaban a harkar kafafen sadarwa sun ce, Tinubu ya bar Abuja a yau Laraba da tsakar rana tare da wasu manya daga cikin masu temaka masa.
Sanarwar ta ce, Tinubun zai yi amfani da damar tafiyar ne wajen sake tantance tsarukansa na karbar mulki tare da mataimakan nasa a inda ba zasu samu damuwa ba.
Sai dai kuma, a jiya ne jaridar SAHARA REPORTERS ta rawaito cewa, Tinubun zai koma Faransa domin likitocinsa su duba lafiyarsa don ya kara samun kwari domin taron ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa.
Jaridar ta kuma labarto cewa, Tinubun ya je Lagos a karshen watan Afrilu inda ya gana da likitocin da suka biyo shi daga Faransa domin kulawa da lafiyarsa bayan dawowarsa daga can a ranar 24 ga watan na Afrilu.
Ana dai ta rade-radin cewar, Shugaba Mai Jiran Gadon ba shi da koshin lafiyar da zai iya jurewa wahalhalun bukukuwan karbar mulki har sai ya samu temakon kulawa daga likitocinsa.