Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Dan Adaidaita Zai Kwashe Watanni 18 A Gidan Gyaran Hali Saboda Batan Babur

Wata kotun majistare da ke Jos, a jiya Juma’a, ta daure wani matshi direban adaidaita sahu, dan shekara 28 mai suna Sagir Abubakar saboda bacewar babur din da aka ba shi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya rawaito cewa, alkalin kotun, Shawomi Bokkos ya daure Sagir ne bayan Sagir din ya amsa laifinsa.

Alkalin ya ce, an yanke hukuncin ne saboda ya zama izina ga wadanda ake baiwa amanar dukiya suna wasa da ita.

Hukuncin da aka yankewa Sagir na da zabin tara ta naira dubu goma ko kuma debe watanni shida a gidan gyaran hali.

Haka kuma an umarce shi da ya biya kudin babur din da ya bata a wajensa naira dubu dari biyu da hamsin da uku ko kuma ya debe shekara guda a gidan gyaran hali.

Tun a farkon shari’ar dai, Dansanda mai shigar da kara, Inspector Ibrahim Gokwat, ya fadawa kotun cewa, wani mai korafi mai suna Balarabe Lawan ne ya shigar da korafin a ofishin yansanda na ‘C’ Division da ke Jos a ranar 3 ga watan Afirilu.

Dansandan ya bayyana cewa, an baiwa mai laifin babur din adaidaita sahu ne da darajarsa ta kai naira dubu dari hudu domin yin sana’a, amma ya kasa kulawa da shi saboda sakaci.