Gwamnatin Jihar Kano ta dawo karbar takardun ‘yan asalin jihar wadanda suka cancanci samun tallafin zuwa karin karatu.
Gwamnatin jihar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar, Malam Sunusi Bature ya sanya wa hannu ranar Juma’a a Kano.
Sanarwar ta ce, ana bukatar dukkan wadanda suka cancanci samun tallafin yin karatun gaba da degree na farko a kasashen waje da kuma cikin Najeriya a shekarar karatu mai kamawa ta 2023/2024.
“Duk wanda ya cancanci morar tallafin dole ne ya zama dan asalin Jihar Kano mai degree na farko a daraja ta farko wato 1st Class ko daidai da shi daga jami’ar da aka amince da ita, sannan kuma ya kasance yana da koshin lafiya ta yin bulaguro da kuma daukar karatu.
“Tallafin karatu na karshe (a jihar) shine na shekarar 2015 lokacin gwamnatin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda aka dau nauyin masu 1st Class su 503 aka tura su kasashe daban-daban har 14.
“Bayan shekaru takwas ba tare da an bayar da tallafin karo karatu ba a gwamnatin da ta gabata, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya amince da dawo da tsarin baiwa dalibai damar karo karatu a kasashen waje da cikin Najeriya, farawa daga shekarar karatu ta 2023/2024,” in ji sanarwar.
NAN