Daga: Ahmed Ilallah
A bana ma Jihar Jigawa na daga cikin jihojin da za su fuskanci ambaliyar ruwa. Gashi kuma har yanzu mutanen da suka fuskanci ibtila’in ambaliyar bara, basu fita daga yanayin da suka samu kan su ba.
Karamar Hukumar Hadejia tafi kowace Karamar Hukuma shiga hadari a duk ambaliyar ruwan da a ka samu a baya. Bayan zahirin masifar ambaliyar, kasan cewar garin Hadejia a matsayin headquarters ta kussan kananan hukukomi goma be sha, ba kawai na Jigawa ba, harma da makwabtan jahar na Bauchi da Yobe.
Hadejia ta sha fama da yan gudun hojira da masifar ambaliyar ta shafa, tabbas Karamar Hukumar Hadejia, kungiyoyin taimako da Gwamnatin Jaha sun yi bakin kokarin su don rike wannan mutanen, da kuma mutanen gari da wannan bala’in ya shafa.
Shin Mene Ne Shirin Mutane A Bana?
Ko da yake, ga dukkanin alamu Karamar Hukumar Hadejia da ma Jihar Jigawa sun soma kanda garki don yin rigakafin wannan ambaliyar a bana.
Shugaban Karamar Hukumar Hadejia, yana daukan matakan don tun karar wannan yanayi a garin Hadejia, wajen gyaran hanyoyin ruwa da magudanan ruwa, sabunta wasu, tattarawa sa kwashe bola, wannan ba karamin taimakawa zaiyi ba wajen rigakafin hatsarin wannan ambaliyar.
Kokarin Shugaban Karamar Hukumar na aiwatar da aiyukan Gwamnatin Tarayya na ecological funds, wanda zai samar da hanyoyi, yin jinga da magudanan ruwa, ba karamin taimako zai yi ba, wajen kandagarkin wannan ambaliyar.
Haka zalika, aiyukan da Gwamnatin Jaha take yi a fadin jahar Jigawa, na yin jinga da share koguna, zai taimaka mutuka, wajen kawo saukin wannan ambaliyar.

Mene Ne Gudun Mawar Al’ummar Mu?
Kamar yadda kowa ya sani, irin wannan bala’in na ambaliya yafi shafar mu, kai tsaye, yana da kyau, muma mu kiyaye da yin rigafin wannan masifa.
Zai mu yi haka ne wajen kiyaye wa da gyaran mujallan mu, mu daina da kin yarda da toshe hanyoyin ruwa, ku zubar da shara a mugudanan ruwa da muhimman wurare.
Mu bada goyan baya da kuma bin shawarar masana a kan matsalolin muhallan mu.
Allah ya kawo mana da sauki!
alhajilallah@gmail.com