Kuka kan tsananin da aka shiga a dalilin janye tallafin man fetur a Najeriya ya ƙara ƙamari a jiya Litinin, a dai-dai lokacin da Kungiyar Ƙwadago, NLC, ke cewa ta shirya tsaf domin yaƙar matsin tattalin arziƙin da hukuncin da Gwamnatin Tarayya ta yi ya jawo ga ƴan Najeriya.
Haka su ma ma’aikatan jami’a ƙarƙashin Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’a a Najeriya, SSANU; reshen Ƙungiyar Malaman Jami’a, ASUU na Jami’ar Lagos; Tarayyar Malaman Jami’o’i, CUA da kuma masu zanga-zanga ƙarƙashin Gamayyar Ƙungiyoyin Ci Gaban Al’umma a Jihar Edo, sun koka kan cire tallafin man fetur ɗin da matsatsin da hakan ya jawo.
Ƙungiyoyin sun koka kan yanayin da ake ciki, suna masu cewa, cire tallafin ba a yi ciking basira ba.
Mataimakin Sakataren NLC na Ƙasa, Chris Onyeka ya ce, Kwamitin Gudanarwa na ƙungiyar zai zauna zama na musamman a yau domin ɗaukar mataki.
Ya ce, dukkan wasu batutuwa da suke tattare da halin ƙuncin da talaka ke ciki saboda tsadar man fetur, sune zasu mamaye abubuwan da za a tattauna a zaman.
Ya ƙara da cewa, zasu yi kira ga Gwamnatin Tarayya a matsayin dama ta ƙarshe, domin a baya sun ba ta lokaci domin samar da gyara da sauƙaƙawa ƴan Najeriya, sai dai kuma gwamnatin ba tai amfani da damar ba, inda ya ce sun shirya tsaf domin mayar da martani a kan hakan.
Su ma Ƙungiyar Ƴan Kasuwa, TUC, sun kushe tsarin baiwa gwamnatocin jihohi damar fito da hanyoyin ragewa ƴan ƙasa raɗaɗin janye man fetur ɗin.
