Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

CIRE TALLAFI: Ma’aikata Zasu Tsunduma Yajin Aiki Ranar Laraba Mai Zuwa A Najeriya

Ƙungiyar Ƙwadago ta shirya tsaf domin tsunduma yajin aiki a duk faɗin Najeriya wanda zai fara ranar Laraba, 2 ga watan Agusta, 2023 kamar yanda jaridar PUNCH ta gano.

Duk da umarnin kotun da ya dakatar da ƙungiyar daga shiga yajin aiki a wanat Yunin da ya gabata yana nan, an fahimci cewa, ƙungiyar ta nuna ba zata naɗe hannunta ba bayan ƴan Najeriya suna suna ci gaba da shan azaba saboda janye tallafin mai.

A watan Yunin da ya gabata ne dai gwamnatin Tinubu ta kai haɗaɗdiyar ƙungiyar ƙwadagon kotu domin kotun ta hanata shiga yajin aikin gamagari biyo bayan janye tallafin man fetur.

A Karanta Wannan: CIRE TALLAFI: Gidajen Mai Sun Fara Shirin Korar Ma’aikata

Duk da kuma gwamnatin ta kafa kwamiti na musamman da zai tattauna da shugabannin ƙungiyoyi ƙwadagon da suka haɗa da Ƙungiyar Ƴan Kasuwa, TUC, da Ƙungiyar Ƙwadago, NLC, kwamitin bai iya cimma komai ba kawo yanzu.

Da yake magana kan lamarin shiga yajin aikin, Ma’ajin Ƙungiyar Ƙwadago na Ƙasa, Hakeem Ambali ya ce, “Eh, mun bayar da wa’adin kwanaki bakwai ga Gwamnatin Tarayya ta ƙarƙare tattaunawa da ƴan ƙwadago ko kuma ta fuskanci yajin aiki.”

A jiya Talata, TASKAR YANCI ta rawaito cewa, NLC zata yi ganawa ta musamman domin ɗaukar mataki kan halin ƙuncin da ƴan Najeriya ke ciki a sanadiyyar janye tallafin man fetur.

Sai dai har kawo wannan lokaci, ba a ji komai daga bakin Shugaban NLC, Joe Ajaero game da sakamakon zaman nasu na jiyan, amma wani daga cikin jagororin ƙungiyar ya bayyana cewa, nan ba da jimawa ba ƴan Najeriya zasu ji matakan da ƙungiyar ta ɗauka.