Gwamnatin Tarayya ta amince da ƙarin alawuns na hazard ga ma’aikatan lafiya da ba na asibitoci ba a fadin ƙasar nan.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne a sanarwar da ta raba mai ɗauke da kwanan watan 26 ga Yuli, 2023, wadda Shugaban Hukumar da Alabashi da Kuɗin Shiga ta Ƙasa, Ekpo Nta ta sanyawa hannu.
Sanarwar an mata take da, “Sake Fasalin Alawun na Hazard ga Ma’aiktan Lafiya da ba na Asibitoci ba Waɗanda ke Kan Tsarin COMESS da CONHESS.”
Labari Mai Alaƙa: CIRE TALLAFI: Gidajen Mai Sun Fara Shirin Korar Ma’aikata
Sanarwar ta nuna cewa, alawuns na hazard ga ma’aikatan lafiyar da ke kan tsarin CONHESS ƴan matsayin grade lavel na ɗaya zuwa na biyar an ƙara shi daga naira dubu biyar zuwa naira dubu goma.
Haka kuma waɗanda suke kan wannan tsarin albashi na CONHESS daga grade level na shida zuwa na sha biyar an ƙara musu daga naira dubu goma zuwa naira dubu goma sha takwas.
Shima alawuns na hazard ga ma’aikatan da ke kan tsarin albashi na CONMESS ƴan grade level na ɗaya zuwa na goma, an ƙara musu daga naira dubu goma zuwa naira dubu goma sha takwas.
Hukumar ta bayyana cewar, ƙarin alawun ɗin ya fara aiki tun daga ranar 1 ga watan Yuni, 2023.
