Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Za A Iya Gyara Rayuwa A Ci Ribarta Ta Hanyar Lura Da Abubuwa Biyar

Daga: Aliyu M Ahmad

Idan kana karanta rubutun nan, ɗauko biro da takarda, ko ka buɗe ‘WPS’ ko wani ‘word processor app’, ko ‘notepad’ na wayarka:

1. Ka tracking na routines dinka, daga asuba zuwa dare lokacin da kake shirin bacci, me da me ka yi. Me ka cimma a yau, mene ne (kuma) ka yi niyyar yi a yau, ba ka samu ka yi ba.

2. Ka auna auyukanka na ɗa’a, da na kauce hanya da ka yi, ka auna alaƙarka da Ubangijinka. Misali, ka sami dukkan sallolin yau a jam’i? Ka yi gulmar wani, ko ka yi ƙarya, ko yin wani aikin assha?

3. Ka auna yanayin mu’amalarka da mutane a yau.

Rubutu Mai Alaƙa: Mece Ce Wayewa?

4. Ka auna riba ko faɗuwa da ka samu a wajen aikinka.

5. Ka rubuta me kake burin yi a gobe, daga tashi daga bacci zuwa lokacin yin bacci.

Don Allah! Ka gwada haka na kwana 10, ‘just for a trial’, za ka yanda rayuwarka za ta canja in sha Allah.

Idan ka kammala ‘tracking routines’ ɗinka, kar ka manta, ka yi alola, ka yi addu’a, ka yi bacci. Idan ka tashi, kar ka manta da ka gama tsara ‘scheduling’ me za ka yi gobe.

Daga: Aliyu M Ahmad

#RayuwaDaNazari