Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA ta ce, akwai aƙalla ƴan Najeriya miliyan 14 da dubu 300 da ke ta’ammuli da miyagun ƙwayoyi.
Kwamandar Hukumar ta Jihar Ogun, Ibiba Odili ce ta bayyana hakan lokacin ƙaddamar da shirin Yaƙi da Ta’ammuli da Miyagun Ƙwayoyi jiya Asabar a Abeokuta.
Ta bayyana cewa, waɗanda suke cikin harkokin ta’ammuli da miyagun ƙawayoyin, ƴan tsakanin shekarun 15 zuwa 64 ne a duniya, inda ta ƙara da cewa, an samu mata da dama sun shiga harkar, inda ake samun mace ɗaya a duk mutum huɗun da aka samu da mummunan aikin.
Ta kuma bayyana cewa, mafi yawan kayan mayen da ake ta’ammuli da su a Najeriya ita ce wiwi, wadda abin takaici aka fi noma ta a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.
