Wasu ƴanbindiga sun kashe manoma aƙalla shida ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Izala, Malam Yakubu Bugai a Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.
Haka kuma, an rawaito cewa, ƴanbindigar sun kuma yi garkuwa da mutane sama da arba’in a lokacin da suke aiki a gonakinsu.
Labari Mai Alaƙa: Sojoji Sun Kashe Ƴanta’adda 59, Sun Kama 88
Shugaban Ƙungiyar Ci Gaban Masarautar Birnin Gwari, Ishaq Kasai, a jawabin da ya fitar yau Asabar ya ce, lamarin ya faru ne a ranar Larabar da ta gabata.
Har zuwa lokacin da ƴanbindiga suka kashe shi, Malam Yakubu Bugai, ginshiƙi a Gidauniyar Temakawa Marayu ta Birnin Gwari, wadda take temakawa dubunnan marayun da waɗanda harin ƴanbindiga ya rutsa da su suka mutu suka bari.
