Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

TANTANCE MINISTOCI: Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Takurawa Wike Ba – Akpabio

Shugaban Majalissar Dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana dalilin da ya sa sanatocin ba su takurawa tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike ba a lokacin da suka tantance shi domin a naɗa shi minista.

Akpabio ya bayyana ƙwarewar Wike a matsayinsa na gwamna da kuma kasancewarsa tsohon minista a gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan a matsayin abin da ya sa sanatocin suka ƙayale shi ya wuce.

A lokacin tantancewar dai, an buƙaci tsohon gwamnan Rivers ɗin da yai gaisuwa kawai ya wuce bayan ya karanta bayanansa, sannan Sanata Barinada Mpigi na PDP daga Jihar Rivers ya buƙaci hakan.

Da ma dai Wike ya taɓa bayyana gaban Majalissar Dattawa inda aka tantance shi ya zama minista a zamanin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan.

Akpabio ya bayyana cewa, tun da ya taɓa zama minista a baya, babu buƙatar a yi masa wasu tambayoyi masu yawa.