Ƙungiyoyin ƙwadago sun nuna rashin gamsuwarsu da gaskiyar tsare-tsaren tallafin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya faɗa a jawabin da yai wa ƴan Najeriya kan magance matsalolin da tsare-tsaren gwamnatinsa suka jawowa ƴan ƙasa.
Ƙungiyoyin sun tabbatar da cewar zasu aiwatar da zanga-zangar da suka shirya yi kan janye tallafin man fetur, inda suka ce, abin da ya faɗawa ƴan Najeriya abu ne na rashin tabbas duba da cewar ya shafe watanni biyu kenan a kan mulki.
Sun bayyana cewa, har yanzu babu wani gamsasshen tsarin da zai kawowa ƴan ƙasa sauƙin rayuwa daga tsare-tsaren Tinubun.

A jawabin da yai wa ƴan ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce, gwamnatinsa na bibiyar tasirin canjin kuɗi da hauhawar farashin mai da alƙawarin ɗaukar mataki a lokacin da ya dace.
To sai dai kuma a jawabin da yai bayan zaman tattaunawa da Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Samar da Tallafi a Fadar Shugaban Ƙasa, Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago, Joe Ajaero ya ce, shirin da a kai na fitowar ma’aikata domin gudanar da zanga-zangar lumana daga gobe Laraba yana nan daram.
Da yake musanta zargin wasu na cewa, ɓatagari kan iya amfani da zanga-zangar wajen abubuwan da ba su dace ba, Ajaero ya ce, ba a taɓa samun hakan ba a zanga-zangar ƴan ƙwadago, inda ya ce, haƙƙin jami’an tsaro ne su kare ma’aikata yayin zanga-zangar.