Daga: Kabiru Zubairu Birnin Kudu
Ba mu so a zo ga nan ba, mun so a ce gwamnati ba ta jefa mu cikin yanayin neman tallafi ba, a nawa ganin kamata yai a ce mu muke tallafa mata da lokacinmu wajen yin aiki da biyan haraji, to amma an taƙarƙare an kassara mu ana kuma ƙara kassaramu – har mun fara gajiya da kukan neman tallafi.
Ban ce fa ba ya komai ba, amma ai ko an ce yanayi ɗin ai jiya i yau, ko ma wani lokacin wasu su ce gwara jiya. Akwai abubuwan motsawa da ya tashi talakan Najeriya tsaye ba ya iya rintsawa, waɗanda ya kamata a ce su irinsu Maigirma Gwamna Namadi na jiharmu sun motsa domin taya talakan jimami da kuma fito masa da hanyoyin samun sauƙi.
Muna dai jin labari a maƙota, kamar Yobe, Borno da Adamawa, Akwai wasu ma a ɗan can nesa da mu da suke ƙoƙartawa. Na san akwai da yawa a jihohi da ba su yi komai ba a wannan ɓangare, amma da yawansu da ma can su da sauran jini a jikinsu, mu kuma Jigawa mun yi ƙaurin suna a talauci da ƙwalawa. Don haka ina ganin ko gwamnanmu bai riga kowa fitowa da hanyoyin samar da sauƙi ga talaka ba a wannan ƙwalawa da ake ya kamata ya zama na biyu ko na uku – sai dai matsalar ko ɗuriyar kwamiti a kan lamarin ma ba ka ji.

Ya kamata Maigirma Gwamna ka yunƙura ka yi abubuwan da za su ragewa ƴan jiharka raɗaɗin janye tallafin man fetur. Ka samar da sauƙi a sufuri, ka samar da motocin haya na jiha, a karɓi rabin kuɗi a wajen fasinja. Ƴan kasuwa, manoma da ma’aikata suna matuƙar buƙatar hakan. Da yawa sun dena zuwa sari kasuwanni saboda lissafin ya shige musu duhu. Da yawa da kyar suke zuwa gun aiki, wasu ma ba sa iya zuwa kwata-kwata an sa su fakewa da jinya ko uzurin da babu. Manoma da yawa gonakinsu sun zama saura saboda ninkuwar kuɗin zuwa gonakin.
Allah Ya temakeka, ya kamata ka yi kamar kana yi gaskiya. Kar ka dogara da tallafin da zai zo daga Gwamnatin Tarayya, wannan daban naka ma daban. Nakan ma zai fi amfani in dai aka yi shi yanda ya kamata.
Daga: Kabiru Zubairu Birnin Kudu
Hurriyah Activist