Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗau Matakin Ba Aiki Ba Albashi A Kan Likitoci Masu Yajin Aiki

Gwamnatin Tarayya ta umarci shugabannin manyan asibitocinta da su yi amfani da tsarin ba aiki ba albashi a kan mambobin Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya, NARD.

Gwamnatin ta kuma buƙaci dukkan asibitocin da su lura da rijistar bayanan zuwa aiki ga likitocin waɗanda ke son ci gaba da aikinsu.

Wata wasiƙa da wakilin PUNCH ya samu a jiya Alhamis wadda Ma’aikatar Lafiya ta Ƙasa ta rubutawa shugabannin asibitocin Gwamnatin Tarayya da ke faɗin Najeriya ce ta tabbatar da umarnin.

Wasiƙar da ke ɗauke da sa hannun Daraktan Al’amuran da Suka Shafi Asibitoci, Dr. Andrew Noah na ɗauke da kwanan watan 1 ga watan Agusta, 2023, kuma an mata take da “Ci Gaba da Yajin Aikin Likitoci Masu Neman Ƙwarewa: Aiwatar da Tsarin ba Aiki ba Albashi na Gwamnatin Tarayya.”

Ƙungiyar NARD dai ta fara yajin aiki ne a ranar 26 ga watan Yuli, 2023, domin neman biyan buƙatunta, yajin aikin da ya samo asali daga gazawar gwamnati na biya mata buƙatun har wa’adin makonni biyun da ƙungiyar ta bayar ya ƙare.

Likitocin dai na buƙatar aiwatar da tsarin dena rage darajar shaidarsu da Kwalejojin Bayar da Shaidar Karatun Gaba da Digiri na Lafiya ke yi, da gaggauta biyansu albashin da suke bi, da kuma aiwatar da tsarin albashin CONMESS a kansu da sauran buƙatu.

Da yake mayar da martani kan wasiƙar, Babban Sakataren Ƙungiyar NARD, Dr. Kelechi Chikezie ya ce, ba su yi mamakin ganin umarnin ba, inda ya ƙara da cewa, shugabannin ƙungiyar zasu haɗu domin samun matsaya a kan batun.