Wani mazaunin Karamar Hukumar Hadejia mai suna Ahmed Haruna wanda aka fi sani da Furya Atafi, ya bayyana shugaban Karamar Hukumar Hadejia, Hon Abdulkadir Umar Bala TO a matsayin abin koyi ga jagorori.
Ya bayyana hakan ne a wata tattaunarsa da wakilin TASKAR YANCI kan kiran da shugaban Karamar Hukumar Hadejia ya yi ga Kungiyar NURTW reshen Tsohuwar Tashar Hadejia, na su samar da sauki ga matafiya, a yayin da ake tsaka da tsadar sufuri wanda janye tallafin man fetur ya kara ta’azzarawa.
Ya bayyana cewa “Harkar sufuri abu ne da ya taba komai, kuma an duba guararen da al’umma suka fi zuwa, aka rage kudin motar (Kano da Gumel). Kuma talakawa ne za su amfana da ragin”.
Ya kuma yabawa Kungiyar NURTW kan amasa kiran shugaban karamar hukumar.

Ya kuma kara da cewa “Ya kamata sauran jagorori, har Mai Girma Gwamna Malam Umar Namadi su kwaikwayi yunkurin Shugaban Karamar Hadejia na ragewa al’umma radadin janye tallafin man fetur saboda yanayin da janye tallafin ya jefa al’ummar kasarnan a ciki”.
Shima wani dan kasuwa mai zuwa Kano akai-akai, Malam Umar Muhammad, ya bayyana cewa, “Ai ragi ko yaya yake a wannan lokaci yana da dadi kuma muna godiya. Allah ya kara masa tausayi”.
Shi kuwa Shugaban Kungiyar Direbobin Motocin Haya, NURTW, reshen Karamar Hukumar Hadejia, Alhaji Sabo Innani, ya bayyana farincikinsa kan abin da ya ce aikin alkhairi suka yi a lokacin da ake tsananin bukatarsa.
Alhaji Sabo Innani, ya ce “Sama da shekara hamsin ina wannan aiki, amma ban taba yin abin da na ji dadinsa ba kamar wannan rage kudin mota da muka yi.
Ya kara da cewa “saboda wannan ragin da muka yi, na samu sakon godiyar al’umma daban-daban; shugabanni, malamai, hakimai, shugabancin ‘yan kasuwa da ma’aikata”.
In za a iya tunawa, a makon da ya gabata ne muka rawaito muku cewa Shugaban Karamar Hukumar Hadejia, Alhaji Abdulkadir Umar Bala T O, ya yi kira ga NURTW reshen Karamar Hukumar Hadejia da su nemo hanyar sassauta wa fasinjoji tsadar sufuri a lokacin da ake tsaka da tsadar sufuri saboda cire tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ta yi.