Majalissar Sanatoci ta kammala tantance mutane 45 cikin 48 da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tura mata a ƙoƙarinsa na naɗa su ministoci.
Sanatocin sun tabbatar da amincewarsu da mutane 45 ɗin ne a jiya Litinin 7 ga watan Agusta, 2023.
Uku cikin waɗanda shugaban ƙasa ya miƙa sunayensu ba su sami tsallakewar tantancewar sanatocin ba har kawo wannan lokacin saboda zarge-zargen tsaro a kansu, sun haɗa da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, Stella Okotette daga Jihar Delta da Abubakar Danladi daga Jihar Taraba.
Sanar da amincewar sanatocin dai na zuwa ne cikin sama da mako guda bayan Shugaba Tinubu a ranar 27 ga Yuli, 2023, ya miƙa jerin sunayen farko ga majalissar adomin tantancewa.

Ministocin da sanatocin suka aminta da su sune:
- Abubakar Kyari (Borno)
- Abubakar Momoh (Edo)
- Nyesom Wike (Rivers)
- Engr Joseph Utserv (Benue)
- Senator John Owan Enoh (Cross River)
- Hon Bello Mohammad (Sokoto)
- Mohammed Badaru Abubakar (Jigawa)
- Amb. Yusuf Maitama Tuggar (Bauchi)
- Uju Kennedy Ohaneye (Anambra)
- Hon. Olubunmi Tunji-Ojo (Ondo)
- Nkieruka Onyejeocha (Abia)
- Dr Betta Edu (Cross River State)
- Imaan Sulieman Ibrahim (Nasarawa)
- David Umahi (Ebonyi)
- Adebayo Olawale Edun (Ogun)
- Arch. Ahmed Musa Dangiwa (Katsina)
- Chief Uche Geoffrey Nnaji (Enugu)
- Mr Dele Alake (Ekiti)
- Waheed Adebayo Adelabu (Oyo)
- Mohammed Idris (Niger)
- Prof Ali Pate (Bauchi)
- Dr Doris Anite Uzoka (Imo)
- Lateef Fabemi SAN (Kwara)
- Rt Hon Ekperikpe Ekpo (Akwa Ibom)
- Hannatu Musawa (Katsina)
- Ibrahim Geidam (Yobe)
- Aliyu Sabi Abdullahi (Niger)
- Hieneken Lokpobiri (Bayelsa)
- Alkali Ahmed Saidu (Gombe)
- Dr Tanko Sununu (Kebbi)
- Atiku Bagudu (Kebbi)
- Bello Matawalle (Zamfara)
- Adegboyega Oyetola (Osun)
- Simon Bako Lalong (Plateau)
- Abdullahi Tijani Muhammad Gwarzo (Kano)
- Bosun Tijani (Ogun)
- Dr Mariya Mahmoud Bunkure (Kano)
- Dr Iziaq Salako (Ogun)
- Dr Tunji Alausa (Lagos)
- Lola Ade-John (Lagos)
- Prof Tahir Mamman SAN (Adamawa)
- Zephaniah Jisalo (FCT)
- Uba Maigari Ahmadu (Taraba)
- Prince Shuaibu Abubakar Audu (Kogi)
- Festus Keyamo SAN (Delta)