Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Amurka Ta Ce In Aka Takura Mata Zata Mamayi Nijar

Ƙasar Amurka ta yi gargaɗi ga sojojin da ke mulki a Nijar da cewar, matuƙar ba a dawo da bin kundin tsarin mulkin ƙasar ba, to zata mamaye ƙasar.

Mai Riƙon Muƙamin Mataimakiyar Sakatariyar Harkokin Waje ta Amurka, Victoria Nuland ce ta bayyana hakan a wata ganawa ta musamman da manema labarai ta waya a jiya Talata.

Ta bayyana cewa, har yanzu akwai abubuwa da dama a ɓangarori daban-daban kan yanda ya kamata tsarin tafiyar da lamarin ya kasance.

Saboda haka Amurka zata ci gaba da lura da abubuwan, sannan kuma akwai buƙatar su ci gaba da tattaunawa da kuma tuntuɓar abokan hulɗa na yankuna kan batun.

Victoria ta ce, “Saboda haka zamu ci gaba da lura da abubuwan, amma mun san iyakokinmu na doka, haka kuma na yi bayani ƙarara ga su mutanen (sojojin Nijar) waɗanda suka jawo wannan, cewar, ba wai buƙatarmu ba ce mu je can, amma zasu iya takura mu ga kaiwa ga hakan.”

“Kuma mun ce musu ya kamata su zama masu lura sannan su ji kiranmu su yi ƙoƙari su sansanta lamarin ta hanyar diflomasiyya sannan su dawo da bin tsarin kundin tsarin mulki.”

Victoria ta kuma ce, Shugaban Ƙasa Joe Biden na yawan tuntuɓar Shugaban Ƙasa Tinubu, Shugaban ECOWAS da Shugaban Ƙungiyar AU Faki, tare da sauran abokan hulɗa na Turai waɗanda suke tare da su musamman a yaƙi da ta’addanci a Nijar.

Ta ƙara da cewa, duk waɗannan abubuwa da suke yi suna da alaƙa da manufarsu ta bunƙasa demokaraɗiyya a duniya, saboda haka ba su ji daɗin ganin abun da ke faruwa da demokaraɗiyyar ba a Nijar.