Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Tinubu Ya Amsa Cewar Akwai Kurakurai A Takardun Karatunsa Na Jami’ar Jihar Chicago

Shari’ar da ɗan takarar jami’iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Atiku Abubakar ya shigar ya neman Jami’ar Jihar Chicago ta bayyana bayanan karatun Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a cikinta ya ɗauki sabon salo, inda Tinubu ya karɓi cewar akwai kura-kurai a takardun.

Lauyoyin Tinubu, a yayin mayar da martani ga buƙatar Atiku, sun ɗora laifin kura-kuran da ke kan takardun a kan ma’aikacin daɗaɗɗiyar jami’ar mai shekaru 156.

Kutun Yanki ta Amurka ta Yankin Arewacin Illinois dai ta bai wa Tinubu wa’adin ranar 23 ga Agusta (jiya kenan) da ya gabatar da bayanai kan dalilin da ya sa ya hana a nunawa mai shigar da ƙara, Atiku Abubakar takardunsa.

A ƙoƙarin biyayya ga umarnin kotun, Lauyan Tinubu ya ce, wani ma’aikacin jami’ar da ba a tantance ba ne ya yi kuskure a kan kwanan watan da makarantar ta bayyana a shaidar karatun Tinubu da ta bayar kwanannan, da kuma bayanin lokacin da ya kammala karatu a jami’ar.

Atiku dai ya buƙaci jami’ar da ta bayyana bayanan karatun Tinubu, waɗanda a ganinsa za su yi maganin ƙudunƙudunar da ke tattare da takardun karatun da Tinubu ya ke cewa ya mallaka.

Akwai maganganu da dama kan ingancin takardun da Tinubu ya gabatarwa Hukumar INEC lokacin da ya ke neman takara da kuma takardar da ta zagaya tana nuni da cewar Jami’ar Chicago ta ɗauki ɗaliba mace a shekarun 1970 mai suna Bola Tinubu wadda aka haifa a ranar 29 ga watan Maris, 1954.

KARANTA WANNAN: El-Rufai Ya Haƙura Da Muƙamin Minista, Ya Tura Sunan Madadinsa

Yayin da shi kuma Tinubu yana bayyana cewar an haife shi ne a ranar 29 ga watan Maris, 1952 sannan kuma a baya ya sha bayyana cewar an haife shi ne a 1954.

A shekarar 1999, lokacin da Tinubu yake neman zama gwamnan Lagos ya bayyana cewar ya halarci waɗansu makarantu a Najeriya, wadda a cikinsu akwai Governmen College Ibadan, wadda daga bisani ya janye iƙirarin ya yi ta.

A ƴan kwanakin baya ma, Tinubu ya janye shaidar kammala karatun primary da secondary daga bayanansa, bayan an gano cewar makarantun da ya ce ya yi a takardar INEC ta CF001 ta shekarar 1999 babu su kwata-kwata a Najeriya.

Buƙatar Atiku ga Jami’ar Jihar Chicago ta kuma haɗa bayyana karatun da Tinubu ya cewa jami’ar ya yi lokacin da yake buƙatar jami’ar ta ɗauke shi a matsayin ɗalibi.

Atikun dai na zargin Tinubu ne da gabatar da bayanai mabanbanta ga Najeriya a lokacin yin takara da waɗanda ya gabatar ga Jami’ar Jihar Chicago lokacin da yake neman karatu, abun da ke nuni da rashin gaskiya a ɓangaren bayanan na Tinubu.