Ƙananan Hukumomi 27 na Jihar Jigawa sun gaza shigar da a ƙalla naira biliyan 3.2 na gudunmawar fansho tsawon shekaru kamar yanda jaridar PREMIUM TIMES ta gano.
Wasu takardu na gwamnati da jaridar ta samu sun bayyana cewar, ƙananan hukumomin ba su shigar da kuɗaɗen fanshon da ya hau kansu ba a shekarun 2014, 2015, 2019, 2020 da kuma 2021.
Takardun sun kuma nuna cewar, gazawar ƙananan hukumomin na shigar da waɗancan kuɗaɗe ya jefa asusun ƴan fansho na jihar cikin mawuyacin hali.
Bayanan takardun sun nuna cewar, kuɗaɗen da aka biyo ƙananan hukumomin guda 27 na gudunmawar kaso 17 cikin 100 daga watan Satumba na 2014 zuwa watan Mayu na 2015 ya kai naira biliyan 1.25.
Haka kuma, a shekarar 2019, kuɗaɗen da ba a shigar ba sun kai naira miliyan 254.6; sai kuma shekarar 2020 da aka gaza shigar da naira miliyan 795; A shekarar 2021 kuma aka gaza shigar da naira miliyan 920.9, Abin da ya sa jimillar kuɗaɗen suka tashi a naira biliyan 3.2.
Abin Da Dokar Fansho Ta Jigawa Ta Ce
Ita dai dokar fansho ta Jihar Jigawa, a sashi na 4 ta tilasta cewar duk wani ma’aikaci da ake iya biyan fansho bayan kammala aiki, za a ciri kaso 8 cikin 100 na gundarin albashinsa, yayin da ita kuma jiha ko ƙaramar hukumar da yake yi wa aiki za ta bayar da kaso 17 cikin 100 na gundarin albashi a haɗa a asusun fansho a ajjiye.
Dokar ta kuma nuna cewar, ma’aikatan da suka yi ritaya zasu mori kuɗaɗen da aka cira musu matuƙar sun ɗebe aƙalla shekaru biyar suna aiki a kan tsarin.
Su kuma waɗanda ba su kai shekaru biyar suna aikin ba, za a dawo musu da kaso 8 cikin 100 da aka cira musu haɗi da kuɗin ruwan da aka samu a yayin ajjiyar kuɗaɗen.