Ƙungiyar NEXT JIGAWA da tallafin PERL ECP sun shirya Tattaunawa Tsakanin Masu Ruwa da Tsaki da nufin magance matsalar da ta addabi tsarin ma’aikata a Jihar Jigawa.
Tattaunawar da ta haɗa da ma’aikatan gwamanati, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki an gudanar da ita ne a Hotel ɗin Three-Star da ke Dutse a jiya Talata.
Da yake jawabi a wajen tattaunawar, Shugaban PERL ECP na Jihar Jigawa, Comrade Isah Surajo, ya bayyana irin buƙatar gaggawar da ake da ita wajen ganin an ceto aikin gwamnati daga rugujewa a Jihar Jigawa.
Ya ce, idan har ba a gaggauta magance matsalar ba, matsalar zata iya shafar dukkanin wasu ɓangarori na gwamnati, inda ya ƙara da cewar Allah Ya yi wa jihar albarkar mutane masu yawa da hazaƙa da zasu iya cike guraben da ake da su.
A na sa jawabin, Shugaban Ƙungiyar NEXT JIGAWA, Farfesa Haruna Usman Hadejia, ya bayyana irin tsananin buƙatar da Jihar Jigawa ke da ita na gaggauta magance matsalar ƙaranci da kuma ingancin ma’aikata.
Ya yi kira ga gwamnati da ta gaggaunata magance matsalar ta yanda Jihar Jigawa zata samu bunƙasar aiyukan gwamnati sannan a samarwa da matasa aiyukan yi.
KARANTA WANNAN: NA MUSAMMAN: LGs A Jigawa Sun Gaza Shigar Da Kuɗin Fansho Kimanin Naira Biliyan 3.2
Shi ma tsohon Shugaban Ma’ikatan Jigawa, Alhaji Inuwa Tahir, wanda ya samu wakilcin Dr. Tanko Ahmed Garun Gabas, ya bayyana irin ƙalubalen da rashin wadatattun ma’aikata ke haifarwa da kuma yanda za a magance matsalolin.
Ya bayyana ɗibar sabbin ma’aikata, dawo da bayar da horo na musamman, bayar da horo kan amfani da na’ura mai ƙwaƙwalwa da kuma shigar da ƙwararrun waɗanda suka yi ritaya cikin aiyukan gwamnati da kuma bai wa sanya kuɗaɗe a fannin aikin gwamnati a matsayin mafita mafi dacewa wajen magance matsalolin.
Da yake yin jawabin a wajen tattaunawar, Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, wanda ya samu wakilcin Babban Sakatarensa na Sirri, Alhaji Adamu Muhammad Garun Gabas ya ce, gwamnatin Jigawa mai ci ta shirya domin magance matsalolin aikin gwamnati a jihar.
Ya ce, Gwamna Namadi ya riga ya kafa kwamitin da zai duba matsalolin da ake da su tare da tsara hanyoyin magance matsalolin domin samun ci gaban jihar mai ɗorewa.
Ya kuma yabawa ƙungiyar NEXT JIGAWA da PERL ECP bisa nuna damuwarsu kan matsalar ma’aikata da ake da ita jihar, ya kuma yi kira ga mahalarta taron da su goyi bayan gwamnati mai ci wajen mayar Jigawa ingantacciyar jiha.