Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Hadejawa, Auyakawa Da Hausawa Sun Manta Muhimmancin Kujerarsu Ta Wakilci A Abuja

Daga: Ahmed Ilallah

Duk da kasancewar an tsara samun wakilcin al’ummah ne a majalissar dokoki ta kasa, don samun adalci da kuma ganin anyi aiyukan kasa daidai wa daida, bisa sa idon kowane dan kasa ta hanyar wakilin sa a wannan majalissar.

Abin takaici da ban mamaki duk da cewar kujerar wakilcin Hadejia, Auyo da Kafin-Hausa, a wannan karan Hon. Usman Kamfani daga Auyo shike sake wakiltar wannnan al’ummar a karo na uku, amma fa tamkar babu wakilci, domin babu wata nasara ta kamaima da za a nuna na ingancin wannan wakilci.

Wannan yankin fa ya na daga cikin yankin da ke kan gaba wajen shahara ba kawai a Jigawa ba, a ma fadin Nijeriya.

Abin takaicin sun gaza samawa kansu martaba a cikin siyasar kasar nan, kai abin takaici ma wannan yankin na cike da matsalolin da ya kamata hukumomin gwamnati su kawo musu kadu, amma abin ya faskara, domin tamkar basu dama wakili a wannan Majalissa Mai Koriyar Tabarma.

KARANTA WANNAN: Sanata Malam Madori Ya Fi Kowa Temakawa Ɗalibai A Yankin Jigawa Ta Gabas

A misali, tun ambaliyar ruwan bara, hanyar gwamnatin tarayya da ta tashi daga cross ta biyo ta Jabo ta zo Hadejia a karye take, kusanma ba ta buyuwa, wannan hanyar ta hada kananan hukumomin Hadejian da Auyo da kuma Kafin Hausan, amma tari bamu ji Hon. Kamfani yayi ba a kan wannan matsalar.

Kai hatta humbasa da yunkuri da takwarorin sa su ke yi na samawa yara matasa aiyuka, a shekaru takwas da doriya, bamu ga yunkurin Hon. Kamfani ba.

A yau fa babu wani kuduri walau wanda ya shafi mazabar sa ko kuma kasa baki daya, da muke da labarin Hon. Kamfani ya kai wannan Majalissa.

Abin mamakin shin duk tarrin yan boko da yan gwagwarmayar wannan yankin sun yi buris da wannan muhimmin wakilci, wanda a karshe al’umar wannan yankin a ke cusawa cikin mummnan yanayi, wajen samo musu hakkin su a wannan Majalissa.

A yanzu mun shigo Majalissa ta goma, mai dauke da kalubale wanda ya banban ta da na baya, yawan matasan mu wanda basu da aikin yi duk da sunyi karatu.

Yankin nan yana da matsaloli da dama kama da gyaran hanyoyin gwamnatin tarayya da suke wannan yankin.

Ya zama dole mu mike a tsaye bisa adalci dan ceto wannan yankin.

alhailallah@gmail.com