Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Tinubu Ya Karya Dokar CBN Wajen Naɗa Madadin Emefiele, In Ji Wani Lauya

Babban Daraktan Ƙungiyar Wayar da Kan Ƴan Ƙasa kan Ƴancin Kai ta CASER, Frank Tietie ya ƙalubalanci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa karya dokar Babban Bankin Najeriya, CBN kan cire tsohon gwamnan Babban Bankin, Godwin Emefiele, tsofin mataimakan gwamnan da kuma naɗa wasu a madadinsu.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne, Tinubu ya sanar da sunan Dr. Olayemi Michael Cardoso a matsayin sabon Gwamnan Babban Bankin domin tantancewar Majalissar Sanatoci.

Lauya Tietie ya yi zargin cewar, babu wata gamsasshiyar shaidar cewa, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya nemi amincewar Majalissar Sanatoci kamar yanda ya ke a dokar CBN da sauran dokokin da ke da alaƙa wajen cire Emefiele.

Tietie ya bayyana hakan a matsayin rashin bin doka, in da ya ce, Tinubu ya karya dokar CBN ta shekarar 2007 wadda ta ce dole ne sai shugaban ƙasa ya samu amincewar kaso biyu cikin uku na sanatoci kafin ya cire gwamnan CBN.

Ya ce rashin bin wannan ƙa’ida ya sanya sabon naɗin da Tinubu yai a matsayin wanda ya saɓa doka kuma wanda za ai watsi da shi.

Bola Tinubu dai ya dakatar da Emefiele ne a watan Yuni, inda ya kafa hujja da cewar akwai buƙatar a yi bincike kan shugabancinsa, binciken da har yanzu ba a fito da bayanin in da aka kwana a yinsa ba.

A kan tsarin da Tietie ya bayyana a matsayin karya doka, bayan gabatar da sunan Cardoso a matsayin wanda zai maye gurbin Emefiele, Tinubu ya kuma gabatar da sunayen waɗanda za su kasance mataimakan gwamnan Babban Bankin: Mrs. Emem Nnana Usoro, Mr. Muhammad Sani Abdullahi Dattijo, Mr. Philip Ikeazor, da kuma Dr. Bala M. Bello.

THE WISTLER