Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya gargaɗi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Jigawa, JSIEC da ta bayar da dama ga kowacce jam’iyya a zaɓuɓɓukan ƙananan hukumomi da ke tafe a jihar.
Wannan na ƙunshe ne cikin takardar sabunta naɗin Auwalu Muhammad Harɓo a matsayin Shugaban Hukumar ta JISIEC.
An rawaito cewar, gwamnan ya amince da naɗin Harɓo tare da wasu kwamishinoni guda uku na hukumar, bayan Majalissar Dokokin Jihar sun tantance tare da amincewa da su.
KARANTA WANNAN: Gwamnatin Jigawa Za Ta Kafa Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci, Yayin Da Fursunoni 1,576 Cikin 1,718 A Jihar Matasa Ne
Kwamishinoni ukun da aka naɗa su ne Auwalu Shehu Jahun, Ibrahim Ahmed Sani, da kuma Ibrahim Babangida.
Wasiƙar naɗin da ke ɗauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim Mamser ta bayyana cewar, an yi naɗin ne bisa cancanta, ƙwarewa da kuma nagarta.
Wasiƙar da ƙara da cewar, dukkanin naɗe-naɗen sun fara aiki nan take.
Zaɓen ƙananan hukumomi a Jihar Jigawa dai, zai kasance ne a watan Yuni na shekarar 2024 bayan cikar wa’adin shekaru uku na zaɓaɓɓun shugabanni da kansilolin da aka zaɓa a watan Yuni na shekarar 2021 kamar yanda dokar zaɓen ƙananan hukumomi ta jihar ta tanada.