A ƙoƙarinta na magance yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya ta hanyar bunƙasa hanyoyin samun ingantaccen ilimi da rayuwar matasan yankin, Ƙungiyar Tarayyar Turai, EU, ta sanar da ƙarin tallafi na yuro miliyan 5.4 don bunƙasa ƙoƙarin malaman makaranta.
Kwamishiniyar Hulɗa da Ƙasashen Waje ta EU, Jutta Urpilainen ce ta bayyana haka a Abuja a lokacin ƙaddamar shiri kan bunƙasa ilimi da matasan yankin Arewa maso Yamma wanda zai laƙume kuɗi yuro miliyan 40.
Ta ce, an ƙara yuro miliyan 5.4 a cikin shirin ne domin tabbatar da cewar malaman makaranta sun horon da suke buƙata wajen samar wa ɗalibai ilimin da zai ba su damar bayar da gudunmawa wajen magance tarun matsalolin da ke fuskantar Najeriya da nahiyar Afirka gaba ɗaya.
Ta ƙara da cewar, ba a taɓa samun ilimi idan babu malamai, wannan ne dalilin da ya sa suka ɓullo da shirin bunƙasa ƙwarewar malaman makaranta ta yanda za su bayar da gudunmawar da ake buƙata.