Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

DA ƊUMI-ƊUMI: Kotu Ta Shirya Yanke Hukunci Kan Shari’ar Cin Zaɓen Gwamnan Kano

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta shirya yanke hukunci kan ɗaukaka ƙarar da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf yai, yana ƙalubalantar hukuncin Kotun Sauraron Ƙarararakin Zaɓe wadda ta soke nasararsa.

Kotun Sauraron Ƙarararkin Zaɓen a ranar 20 ga watan Satumba ta soke nasarar Abba Kabir Yusuf ta hanyar bayyana cewar ƙuri’u 165,663 cikin ƙuri’un da ya samu na bogi ne.

Kotun ta ce, ƙuri’un wasu ba a sanya hannu da satamfin hukumar INEC  a kansu ba, saboda haka ta bayyana Nasiru Umar Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya ci zaɓen.

Da yake nuna rashin gamsuwarsa da hukuncin, Abba Kabir ya ɗaukaka ƙara yana ƙalubalantar hukuncin, tare da buƙatar kotun ta yi watsi da hukuncin baya.